Majalisar Dokoki, ta tuhumi hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) kan kashe kuɗaɗe masu yawa wajen abinci, ruwa, lemu, da maganin sauro a shekarar 2024.
Kwamitin kuɗi na majalisar ya yi barazanar cire JAMB daga jerin ma’aikatun da za su samu kasafin kuɗi daga gwamnati a shekarar 2025, idan ba ta bayar da cikakken bayani kan wannan kashe-kashen ba.
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
- Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Makaranta Kyauta Ga Dalibai 789,000
Hakan ya faru ne bayan da shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya gabatar da kasafin kuɗin hukumar na 2025 a gaban kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilai.
A cewar Oloyede, JAMB ta samar da kuɗin shiga har Naira biliyan 4 a shekarar da ta gabata, yayin da gwamnatin tarayya ta ba ta tallafin biliyan shida.
Sai dai, Sanata Adams Oshiomhole daga Edo ta Tsakiya, ya tuhumi hukumar kan kashe Naira miliyan 850 kan tsaro, share-share, da feshin maganin sauro, tare da miliyan 600 kan tafiye-tafiyen cikin gida.
“Kun kashe sama da biliyan ɗaya kan abinci da lemu. Shin gwamnati ke ciyar da ku kyauta?
“Wannan ya nuna cewa kuna kashe kuɗin ɗalibai marasa galihu, waɗanda da yawansu marayu ne.
“Haka kuma, kun ce kun kashe miliyan 850 kan maganin sauro. Shin sauro ne suka cinye dukkanin kuɗaɗen?” in ji Oshiomhole.
Ya buƙaci JAMB ta yi cikakken bayani kan wannan kashe-kashe kafin majalisar ta yanke hukunci.