Majalisar Wakilai ta fara gudanar da bincike kan halin da ake ciki game da soke takardar izinin shiga kasar Saudiyya da hukumomin kasar suka yi wa ‘yan Nijeriya 264.
Har ila yau, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakin diflomasiyya da ya dace domin kare martabar al’ummar kasar nan.
- Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Kasar Amurka Domin Gudanar Da Taron Shugabannin Kasashen Sin Da Amurka Da Taron APEC Karo Na 30
- Yajin Aiki: TCN Ya Musanta Rahoton Datse Wutar Lantarki A Fadin Nijeriya
Majalisar ta yi Allah-wadai da soke bizar ‘yan Najeriya 264 da hukumomin kasar suka yi a Saudiyya a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, 2023.
Majalisar ta yanke hukuncin ne bayan amincewa da kudirin da Kama Nkemkanma da wasu mutane hudu suka gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.
Da yake gabatar da kudirin, Nkemkanma ya tunatar da cewa hukumomin Saudiyya sun soke bizar dukkan fasinjoji 264 da jirgin saman Air Peace ya yi jigilarsu zuwa Jeddah daga filin jirgin saman Mallam Aminu Kano a ranar Litinin.
Dan majalisar ya bayyana cewa duka fasinjojin sun bi ta hanyar da ta dace, wanda kuma hukumomin Saudiyya suka sanya ido kai tsaye kafin jirgin ya tashi daga Nijeriya.
Nkemkanma ya ce bayan shiga tsakani da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Saudiyya ya yi, an ce hukumomi sun rage adadin fasinjojin da za a dawo da su Nijeriya daga 264 zuwa 170.
Dan majalisar ya bayyana damuwarsa kan yadda masu ruwa da tsaki suka yi shiru da bakinsu.
Nkemkanma ya ce matakin da mahukuntan Saudiyya suka dauka cin zarafi ne ga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Nijeriya da Saudiyya da har yanzu ke aiki.