Majalisar wakilai ta umarci kwamitinta kan samar da abinci mai gina jiki da wadatar abinci, fitar da amfanin gona da ayyuka, da kwalejojin aikin gona da na cibiyoyi da na kudi da su gudanar da cikakken bincike kan zargin rashin amfani ko kin aiwatar da shirye-shiryen gwamnati da kudaden bangaren noma daga sashi-sashi, hukumomi da shirye-shiryen da manufofin gwamnatin tarayya a wajen ma’aikatar harkokin gona da wadata kasa da abinci.
Wannan na zuwa ne bayan kudirin da Hon. Chike Okafor ya gabatar a yayin zaman majalisar a Abuja.
Ofafor ya lura kan cewa akwai karancin abinci da kuma cutar tamowa a Nijeriya, tare da zargin karkatar da kudaden da aka ware domin aiwatar da shirye-shiryen da manufofin gona da niyyar bunkasa harkokin noma da kayan abinci a Nijeriya.
- Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Minista Da Sanatar Abuja
- Biyan Sabon Haraji: Gwamnati Ta Tsame Kananan Kamfanoni Da Manoma
Ya lura kan cewa gwamnatin tarayya ta yi shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban cikin shekaru takwas da suka wuce ta kashe makuden kudade sama da tiriliyan biyu wajen daukan nauyin shirye-shiryen manufofin noma da manufar wadata kasar da abinci, sai dai kuma zargin karkatar da kudaden da rashin aiwatar da shirye-shiryen na kara fitowa fili ta yadda Nijeriya ke ci gaba da fuskantar karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki.
A cewarsa, rahotonni da kuma zarge-zargen tafka rashawa, karkatar da kudade, da tafka kura-kurai su ne suka mamaye shirye-shiryen gwamnatin ta yadda kudaden da aka ware ba su yi amfanin da aka yi hankoro ba, inda a cewarsa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba da tallafi ga manoma na ‘Anchor Borrowers’ ya rabar da sama da naira tiriliyan I.12 ga manoma miliyan 4.67.
“Shirin NIRSAL ya rabar da sama da naira biliyan dari biyu da sha biyar da miliyan sittin da shiya zuwa yanzu domin saukaka ayyukan gona da kasuwancin noma.
“Bankin masana’antu (BOI) ya fitar da sama da naira biliyan uku ga kananan manoma dubu 22 ta hannun shirin ABCF. Kari kan rancen biliyan 59.4 ga ‘yan kasuwan da ke harkar noma.
“A 2023, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin rancen naira biliyan 5 ta bankin manoma (BOA) makiyaya a fadin kasar nan. A watan Maris na 2024 asusun tallafin harkokin noma na kasa (NADF) ya kaddamar da dawo da shirin biliyan 1.6 domin dakile cuta a ginger da wasu shirye-shirye.”
Ya ce, bayan wadannan akwai shirye-shirye da dama dukka da gwamnati ta samar da nufin shawo kan karancin abinci da wadata kasa da abinci da abinci mai gina jiki, amma abun takaici har yanzu ‘yan Nijeriya na fama da matsalar karancin abin da za su ci da wanda zai gina musu jiki. Don haka ne ya ce akwai bukatar kaddamar da bincike domin gano yadda aka kashe wadannan kudaden ko kuma inda suka makale.
Domin tabbatar da gaskiya da adalci, majalisar ta amince da kudirin tare da tsammanin cewa kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin mako hudu.