ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Dattawa

Kwamitin Majalisar Dattawa na sake duba kundin tsarin mulki na 1999 yana nazarin shawarwari 31 na ƙirƙirar sabbin jihohi, gami da buƙatun Arewa maso gabas (7), Arewa maso yamma (6), da kudu maso gabas (3).

Bayanai sun nuna cewa majalisar ta kuma yi niyyar ba wa ƙananan hukumomi 774 cikakken ‘yancin kai, yayin da za ta yi nazarin kundin dokoki 20 na gyaran shari’a da kafa wa’adin yanke hukunci.

  • Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma
  • EFCC Ta Kama Tsohon Kakakin Majalisar Filato Da Wasu ‘Yan Majalisa 14 Bisa Zargin Almundahana

Wannan ya zo ne daidai lokacin da majalisar ta shirya taron jin ra’ayin jama’a na kwana biyu a shiyyoyi shida na ƙasar don tattara ra’ayoyin mutane kan gyare-gyaren kundin tsarin mulki.

ADVERTISEMENT

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, zai yi nazarin muhimman batutuwa kamar:

1. Ƴancin ƙananan hukumomi

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170

2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe

3. Ƙirƙirar sabbin jihohi

4. Samar da Ƴansandan jihohi

5. Haɗa kai don gudanar da mulki

Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe.

Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa.

Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a:

– Lagos (Kudu maso Yamma)

– Enugu (Kudu maso Gabas)

– Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu)

– Jos (Arewa Tsakiya)

– Maiduguri (Arewa maso Gabas)

– Kano (Arewa maso Yamma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya
Manyan Labarai

Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

November 11, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Manyan Labarai

Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170

November 11, 2025
Rashin Aiki Ga Matasa Babbar Barazana Ce Ga Nijeriya – Obasanjo 
Manyan Labarai

Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika

November 11, 2025
Next Post
Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

Iran Da Isra'ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta - Trump

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

November 11, 2025
HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano

HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Da ‘Yan Ta’adda Sun Fi Sojojin Nijeriya Yawan Makamai – Babachir

‘Yan Bindiga Da ‘Yan Ta’adda Sun Fi Sojojin Nijeriya Yawan Makamai – Babachir

November 11, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170

November 11, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn

November 11, 2025
Rashin Aiki Ga Matasa Babbar Barazana Ce Ga Nijeriya – Obasanjo 

Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika

November 11, 2025
Yadda Muka Zama Bayin ‘Yan Bindiga -Mazaunin Wani Kauye

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina

November 11, 2025
An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

November 10, 2025
Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

November 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.