Majalisar Dattawan ƙasar nan ta tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan, mai muƙamin SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a yammacin ranar Alhamis.
Tabbatar da Farfesa Amupitan, ta kasance ta hanyar ƙuri’ar murya da ‘yan majalisar suka gudanar bayan kammala tantance shi tare da amsa tambayoyi daga mambobin majalisar na tsawon kusan sa’o’i biyu.
- Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ne ya gabatar da sunan Amupitan, don maye gurbin tsohon shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya sauka muƙamin makonni biyu da suka gabata.
Amupitan, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai zuwa majalisar, ya gabatar da tarihin inda ya yi aiki kafin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar.