A yammacin ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da tantance sunayen ministoci bakwai da shugaban kasa Bola Tinubu ya mika mata domin nada su a matsayin ministoci da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Kudurin Majalisar ya biyo bayan tantance sunayen ministocin da Sanatocin suka yi na tsawon sa’o’i.
- Tattalin Arziƙi: Jega Ya Gargaɗi Nijeriya Kan Amincewa Da Shawarwarin IMF Da Bankin Duniya
- Mene Ne Burin Amurka Wajen Sake Yada Jita-Jitar “Barazanar ‘Yan Leken Asirin Kasar Sin”
Ministocin da aka nada sun hada da Dr. Nentawe Yilwatda, ministar harkokin jin kai da rage talauci; Muhammadu Maigari Dingyadi, Ministan Kwadago da Aiki, da Amb. Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu, Karamar Ministan Harkokin Waje.
Sauran sun hada da Dr. Jumoke Oduwole, Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Idi Muktar Maiha, Ministan kula da kiwon Dabbobi; Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, Karamin Ministan Gidaje, da Dr. Suwaiba Said Ahmad, Karamar Ministan Ilimi.
In ba a manta ba, a cikin wata wasika da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa a makon da ya gabata ya bukaci majalisar ta gaggauta tantance ministocin domin fara aikin lalubo mafita ga halin da kasar ke ciki.