Majalisar Dattawa ta buɗe ofishin Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, wanda hakan ke nuna alamar ƙarshen taƙaddamar da ta daɗe tana yi da Shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio.
A yau Talata 23 ga watan Satumban 2025, ne jami’in tsaron majalisar, tare da haɗin gwuiwar dakarun tsaro, suka sake buɗe ofishin Sanata Natasha, mai lamba 205 a harabar Majalisar Dattawa.
- Majalisar Dokokin Ribas Za Ta Binciki Tsohon Kantoman Riƙo Ibok-Ete Ibas
- Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
Wannan mataki ya dawo mata da cikakken damar shiga harabar majalisar da ofishinta, wanda hakan zai iya bai wa Sanatar damar komawa zaman Majalisar Dattawa lokacin da ‘yan majalisa za su koma bakin aiki a ranar 7 ga watan Oktoban 2025.
Majiyoyi sun ce an ɗauki wannan mataki ne a wani taron shugabancin majalisar da aka yi a ranar Litinin, inda aka tsara cewa shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro, zai gabatar da ƙudiri don a yi uzuri tare da mara masa baya, sai a gabatar da shi a gaban majalisar inda za ta bayar da haƙuri.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ta taɓa shugabantar Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin tafiye-tafiyen ƙasashen waje da Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu, an dakatar da ita na tsawon watanni shida a watan Maris, bayan ta nuna adawa da sauya mata kujera wanda majalisar ta zarge ta da saɓa dokokinta.
Yanzu da aka buɗe ofishinta kafin komawar zaman majalisar, hankali ya karkata kan zaman majalisar na watan Oktoba, don ganin ko za a gabatar da kuɗirin dawowarta, da kuma ko za a tilasta mata ta nemi afuwa kafin ta dawo ta zauna a kujerarta a cikin zauren majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp