A yayin da jama’a ke nuna bacin rai da rashin gamsuwa sakamakon karin farashin man fetur da kuma karancinsa a kasuwanni, majalisar dattawa ta dakatar da binciken lamarin wanda ya haifar da rudani.
Jagoran majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin binciken badakala a bangaren masana’antar man fetur ta Nijeriya, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a farkon makon nan.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Kaduna: Ruftawar Hanya Sakamakon Ambaliyar Ruwa Ta Katse Garuruwa Biyar A LereÂ
A cikin sanarwar da Bamidele ya fitar bai yi bayanin dalilin dage binciken ba, amma ya yi ikirarin cewa an dauki matakin ne domin amfanar da kasar nan da kuma al’ummarta.
Ya kuma bayyana cewa dage binciken ya zama wajibi bisa la’akari da bukatar da ake da ita na kara tuntubar masu ruwa da tsaki a ciki da wajen harkar man fetur da kuma majalisun dokoki domin kara zurfafa bincike a kan lamarin.
Ya ce, “Abubuwan da ke faruwa a kasar nan da suka bukatar dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya su dauki matakin gaggawa.
“Yayin da muke matukar yin nadama kan duk wata matsala da ta shafi al’ummar kasar nan, an yanke wannan shawarar ne saboda amfanin kasa.”
Ya bayyana cewa an dauki kowanne daga cikin wadannan hukunce-hukuncen ne domin bai wa kwamitin wucin gadi damar gudanar da harkokin jin ra’ayoyin jama’a tare da samar da mafita mai dorewa kan kalubalen da ke fuskantar bangaren man fetur na kasar nan.
Majalisar dattawar ta kuma bai wa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa za a sanar da su sabuwar ranar jin ra’ayoyin jama’a nan gaba kadan.
Bincike ya nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki biliyoyin da aka kashe wajen kula da matatun man kasar nan tare da binciko hukumomi da ke kula da kudaden da ake biya ga masu safara da kuma bankado zargin shigo da gurbatattun albarkatun man fetur da dizal mara inganci cikin kasar nan.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa kwamitin wucin gadi ya kammala gudanar da ayyukansa na bincike kafin ya gudanar da taron tattaunawa da shugabannin ma’aikatu da hukumomin da kuma wasu masu zaman kansu a bangaren man fetur na kasar nan.