Majalisar dattawa, a yau Laraba, ta sanar da tsige Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu Mohammed Ali Ndume, a matsayin mai tsawatarwar majalisar bayan amincewa da shawarar tsige shi ta hanyar jefa kuri’a da Sanatocin suka yi.
Hakan ya biyo bayan bukatar da jam’iyyar APC mai mulki ta yi a baya ga Sanata Ndume, na ya yi murabus daga mukaminsa na babban jami’in majalisar dattawa ta 10.
- Kotu Ta Dawo Da Shaibu A Matsayin Mataimakin Gwamnan Edo
- Abba Ya Sake Nada Tsohon Sarkin Gaya Da Wasu Sabbin Sarakuna A Kano
APC ta yi wannan bukata ne cikin wata wasika da ta aike wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zauren majalisar a yau Laraba.
Idan ba a manta ba Ndume ya fuskanci kalubale daga fadar shugaban kasa da kuma jam’iyyar APC, kan sukar da ya yi wa salon mulkin shugaba Bola Tinubu, dangane da yadda al’ummar NIjeriya ke ci gaba da kasancewa cikin halin ni ‘ya-su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp