Majalisar Dattawa, ta hanyar kwamtin kula da kudade na majalisar, ta nuna bacin ranta kan asarar da aka tabka ta Naira tiriliyan 17 biyo bayan damar da aka bayar wajen tattara haraji a shekaru biyar da suka gabata.
Kazalika, majalisar ta kuma shawarci hukumar tattara haraji ta FIRS da ta dakatar da bayar da wannan damar ta tattara harajin.
- ‘Yan Nijeriya Ku Ba Wa Tinubu Ƙarin Lokaci Zai Magance Matsalolin Nijeriya – Gowon
- ‘Yan bindiga Sun Kashe Mutum 6 A Jihar Katsina
Majalisar ta nuna kin aminta da ci gaba da bayar da wannan damar da majalisar ta yi, ta bijiro ne a cikin kasafin kudi na 2024 da hukumar ta FIRS ta gabatar wa da kwamitin kula da kashe kudade na majalisar.
Bugu da kari, shugaban hukumar FIRS Zacch Adedeji ya shda wa kwamtin cewa, hukumar na sa ran za ta tara harajin da ya kai jimlar Naira tiriliyan 19.4 a 2024, sabanin bashin harajin da ya kai Naira tiriliyan 2.7 wanda aka tsara za yi aikin yin hanyiyi da babban bankin Nijeriya zai yi a kasar nan, wanda kuma za a dakar da yin akin.
Shi ma a jwabinsa shugaban kwamitin sanata Sani Musa na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Neja ta gabas ya shedawa shugaban na FIRS, cin zarafin na bayar da damar da biyan harajin, ya haifar da Nijeriya tabka asarar kimanin Naira tiriliyan 17 a shekaru biyar da suka wuce, wanda ya zama wajibi, a dakatar da bayar da wannan damar.
Ya yi nuni da cewa, hasashen da shugaban hukumar ya yi na son tara harajin da ya kai na Naira tiriliyan 19 a 2024 abu ne mai kyau idan aka kwatanta da harajin da hukumar ta tara a 2023 wanda ya kai jimlar Naira 11.16.
Ya ci gaba da cewa, sai dai, majalisar na da yakinin za ka iya tara harajin da kai na Naira tiriliya 30 idan har an samar da matakan fa suka dace.
Har ila yau, Zacch ya shewa kwamitin cewa, don a kare Nijeriya daga rubanya karbar haraji FIRS ta hanyar uin hadaka da kwamtin da shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa, za su rage karbar haraji da ban da ban da suka kai 62 zuwa guda 8, inda ya ce, wannan abun taiakici ne ganin cewa, a Niheriya ayau ana karbar harajin da ya kai ba da ban da ban har guda 62 wanda kuma daga cikin 62, ya kai kashi 97 da ake iya tattarawa.
Ya kara da cewa, tuni kan wannan mun fara tuntubar gwamnonin jihohin kasar nan wanda ya zuwa yau, ba za mu samu sama da takwas zuwa tara na harajin da jihohi da gwamnatin tarayayya, za su tattara ba.
Da yake yin bayani kan takardamar wanzar da tsarin haraji na TCS na gina hanyoyi da CBN zai yi Zacch ya nanata cewa, tun da farko an ware Naira tiriliyan 2.5 ne don yin aikin wanda kuma dole ne a wanzar da aikin, kafin a fara yin wani sabon aikin.
Kan shirin bashin haraji kuwa ya ce, shiri ne mai kyau amma dole ne sai kamfanin NNPCL ya kammala kashe Naira tiriliyan 2.5 da aka ware masa kafin a fara wani sabo.