Majalisar Dokoki ta Ƙasa tana shirin gabatar da ƙudirin dokar da zai ba da shawarar hukuncin kisa ga masu lalata kadarorin ƙasa a Najeriya. Wannan bayani ya fito ne daga Sanata Adamu Aliero, tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya kuma Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya. Sanata Aliero ya jaddada damuwar da ake da ita kan lalata muhimman kayayyakin more rayuwa na ƙasa, ciki har da na’urorin wutar lantarki, da layukan dogo, da kuma filayen jirgin sama.
Haka zalika, Hon. Blessing Onuh, mamba a Majalisar Wakilai, ta yi kira da a sanya kayan kariya domin hana lalata kadarorin gwamnati. Kwanan nan, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta kama wasu da aka samu da manyan motocin da suka ɗauko ƙarafunan titunan jirgin ƙasa da aka sace, wanda hakan ya nuna tsananin matsalar. Ministan Sufuri, Alkali S’aidu, ya danganta karyewar layin dogo da aka samu kwanan nan da irin wannan lalatawa, yana mai jaddada buƙatar inganta matakan tsaro don kare waɗannan kadarori.
- Ana Zargin Tsohon Shugaban Nijar Issoufou Da Yin Sama Da Faɗi Da Kuɗin Sayen Jirgin Sama
- Nakan Noma Hekta 23 Amma Rashin Tsaro Ya Sa Na Koma Hekta Hudu Kacal – Aisha Abubakar
Sanata Aliero ya bayyana cewa Majalisar Dokoki tana shirin ɗaukar mataki mai tsauri don magance matsalar. Ya ce, “Idan zai yiwu, duk wanda aka kama yana lalata kadarorin jama’a, hukuncinsa ya kamata ya kasance kisa. Wataƙila, idan hakan ya faru, zai taimaka sosai wajen rage lalata kayayyakin more rayuwa.” Ma’aikatar Sufuri tare da haɗin gwuiwar hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya da hukumomin tsaro suna kuma ƙoƙarin samar da matakan sa ido don hana lalata kadarorin ƙasa nan gaba.