Majalisar Wakilai ta umarci Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) da ya gaggauta kawo karshen wahalar man fetur da ake fama da shi a kasar nan cikin mako guda.
Umarnin ya biyo bayan wani kudurin gaggawa da dan majalisa Sa’idu Musa Abdullahi (APC, Neja) ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.
- Ba Za Ku Taba Nadamar Zaben APC A Karkashin Mulkina Ba – Tinubu
- Gwamnatin Ebonyi Ta Ba Da Umarnin Kashe Duk Wanda Aka Gani Da BindigaÂ
Da yake gabatar da kudurin, dan majalisar ya ce ’yan Nijeriya a tsawon watannin da suka gabata sun jima suna fama da matsalar man wacce take nakasa tattalin arziki.
Ya ce Hukumar Kula Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta sha kawo dalilai marasa tushe kan abin da ya haddasa wahalar.
Dan majalisar ya ce, “Lokacin da matsalar ta fara ta’azzara a watan Oktoba a Abuja da sauran jihohin Arewacin Najeriya, sai NMDPRA ta bayar da hanzarin cewa ruwan saman da ya shanye gadar Lokoja ne ya gurgunta harkar sufurin man ya kuma kawo wahalar man.”
Yanzu haka dai jihohi da dama ana sayar litar man fetur sama da 300, inda gidajen mai ke ci gaba da tara dogayen layuka saboda tsada da kuma karancin man.
Mutane da dama sun koka kan yadda tsadar da karancin man ke ci gaba da gurgunta harkar kasuwanci da haddasa tsadar kayayyaki.