Sin ta fitar da rukunin farko na hotunan da aka dauka da ingantacciyar na’urar binciken rana ta Kuafu-1. An baje hotunan ne yayin taron manema labarai da ya gudana yau Talata, a cibiyar nazarin kimiyyar samaniya ta kasar Sin.
Na’urar mai dauke da cikakkun sassan fasahohin zamani na binciken rana ko ASO-S, wadda kuma aka sa mata suna Kuafu-1, tana aiki ne kan falakin ta dake da nisan kilomita 720 daga doron duniyar mu, inda take fuskantar rana tun bayan harba ta a watan Oktoba. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)