Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.
Shugabar masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian ce, ta bayyana shirin tsige mataimakin gwamnan a zaman majalisar na ranar Laraba.
- Jami’i: Kasar Sin Za Ta Iya Cimma Burin GDP Na 2024
- EFCC Za Ta Gurfanar Da Masu Motocin Da Aka Kama Da Kayan Abinci A Borno
Aiguobarueghian, ta bayyana cewa adadin ‘yan majalisar da suka rattaba hannu kan takardar ya zarce kashi biyu bisa uku da kundin tsarin mulkin na 1999 ya tanada.
Ta kuma sanar da cewa an gabatar da bukatar tsige shi ne bisa dalilai guda biyu na yin karya da kuma tona asirin gwamnati.
Kakakin majalisar, Blessing Agbebaku, wadda ta amince da karbar koken, ta umarci magatakardar majalisar, Yahaya Omogbai, da ya fara shirye-shiryen fitar da sanarwar tsige mataimakin gwamnan.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, alaka ta yi tsami tsakanin Shaibu da uban gidansa, Gwamna Godwin Obaseki, a watannin da suka gabata kan wanda zai gaji gwamnan.