A safiyar yau Litinin ne majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
Kazalika majalisar ta umurci magatakardar majalisar da ya aike wa da Gwamna Fubara da takardar sanar da shi shirin majalisar na tsige shi.
- Jiragen Yakin NAF Sun Tarwatsa Haramtattun Matatar Mai 7 A Jihar Ribas
- Rikicin PDP A Ribas: Atiku Muke Wa Biyayya Ba Wike Ba
LEADERSHIP ta ruwaito cewa da safiyar Litinin ne Majalisar ta tsige Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Hon. Edison Ehie, domin share filin yunkurin tsige gwamnan.
Gwamna Fubara ya kutsa kai harabar majalisar a yau Litinin yayin da zauren ya rincabe da hayaniya, inda ya yi jawabi ga magoya bayansa, Gwamnan ya ce bai aikata wani laifin da za a iya tsige shi ba har da za a dauki wannan matakin a kansa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa rikicin siyasar da ya kunno kai a jihar ya samo asali ne sakamakon burbushin tsamin dangantaka da ke tsakanin gwamnan da ubangidansa na siyasa, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar kuma a yanzu haka ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom. Wike.