Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da dokar sauya sunan jami’ar kimiyya da fasaha ta Jihar Kano, da ke garin Wudil.
‘Yan majalisar, a zaman da suka yi a ranar Talata, karkashin jagorancin shugaban majalisar, Alhaji Hamisu Chidari, sun amince da sauya sunan cibiyar zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote.
- Sojoji Sun Damke Fakitin Tabar Wiwi 98 A Yobe
- PBOC Ya Lashi Takwabin Inganta Yadda Ake Amfani Da RMB A Duniya Wajen Zuba Jari Da Harkokin Kudi
Hakan ya biyo bayan wata wasika da bangaren zartarwa ya aike wa majalisar a watan Mayu, inda ya nemi amincewar sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUST), Wudil.
Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewa da rahoton da kwamitin majalisar kan ilimi mai zurfi ya yi.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Labaran Madari, (APC-Warawa) ne ya gabatar da kudirin amincewar, inda Nuhu Acika (APC-Wudil) ya mara masa baya.
‘Yan majalisar dai sun kada kuri’ar amincewa da kudirin bayan karatu na uku.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Madari ya bayyana cewa amincewar ta biyo bayan nasarorin da Dangote ya samu da kuma gudunmawarsa mara misaltuwa ga ilimi da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Shugaban majalisar ya umarci magatakardan majalisar da ya mika wa gwamnan jihar kudirin don amincewarsa. Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa, a shekarar 2008 ne tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ya nada Dangote a matsayin shugaban jami’ar, sannan gwamna Abdullahi Ganduje ya sake nada shi a shekarar 2021.