Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, ta sanar da dakatar da dan majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi Arewa, Hon. Hassan Umar a zamanta na ranar Juma’a.
Wannan na cikin sanarwar manema labarai mai kwanan wata da ranar Juma’a 12 ga watan Afrilu, 2024, kuma mai dauke da sa hannun Suleiman Shamaki, magatakardan majalisar.
- Kalau Nake Babu Abin Da Ke Damun Kwakwalwata – Adam Zango
- Ra’ayoyin Kasashen Duniya Game Da Harin Da Iran Ta Kaddamar A Kan Isra’ilaÂ
Sanarwar ta bayyana cewar dan dakatar ne sakamakon wasu kalamai na rashin tsaro da ya yi, da kuma cin zarfi ga shugabancin majalisar kanta da ya haddasa rashin jituwa tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa a jihar.
Bisa ga wadanan zarge zargen ne majalisar dokokin Jihar ta bayar da sanarwar datakar da shi daga zaman majalisar ko gudanar da wani aiki har sai lokacin da majalisar ta bayar da sanarwar janye dakatarwar.
A wata tattaunawa da wasu daga cikin mutanen da dakatacen dan majalisar ke wakiltar a Mazabun Kola- Tarasa da Badariya sun bayyana lamarin da matukar bakin ciki, mummuna kuma a matsayin cin zarafi da kuma yin watsi da tanade-tanaden kundin tsarin mulki wanda ya bai wa kowace mazaba ikon wakilci ta samu mutum a matsayin mamba mai wakiltar wata mazabun a majalisar dokokin jiha ko a tarayya.
“Matakin da majalisar jihar ta dauka na dakatar da dan majalisarmu ba ya bisa ka’ida ta fuskar doka.”
Haka kuma sun jaddada cewa hakan bai dace da dimokuradiyya ba.
Haka zalika sun kara da cewa a iya saninsu wani zababben memba ba shi da ikon bisa ga kudin dokar tsarin mulki na dakatar da shi ko ita wanda aka zaba bisa cancanta a matsayin memba mai wakiltar wasu mazabun a yankin jiha ko na tarayya.
Al’ummar yankin dakatacen dan majalisar suna kira ga gwamnan jihar da shugabannin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki da su gaggauta kawo karshen dakatarwar da aka yi masa.
Haka kuma, dakatarwar da aka yi masa gaba daya ya zama tauye hakkin daukacin mazabun Birnin Kebbi ta Arewa a majalisar kan wakiltar su, wanda ana nufin cewa a halin yanzu ba su da wakilci a zauren majalisar dokokin jihar.
“Bugu da kari muna ganin cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa kuma ba shi da tushe a gaban doka.
“Muna kira ga duk masu hannu da kuma ruwa da tsaki da su shigo tare da tabbatar da cewa an dawo da membanmu mai aiki tukuru ga mazabun Birnin Kebbi ta Arewa a majalisar dokokin Jiha.”