Majalisar dokokin jihar Oyo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Rauf Olaniyan.
Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan da ta yi la’akari da shawarorin da kwamiti mai mutum bakwai a karkashin babban jojin jihar Munta Abimbola suka bayar.
Kwamitin da aka kafa domin su bincike zarge-zargen rashin da’a da ladabi da ake yi wa mataimakin gwamnan.
A cewar Majalisar Dokokin wannan tsigewar ya fara aiki ne nan tare ba tare da bata wani lokaci ba.
Bisa rahoton da kwamitin ya mika wa Majalisar a zamanta na yau Litinin, kwamitin ya tababtar da cewa dukkanin zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan ya aikata su, don haka ne suka bada shawarar a tsige shi.
Cikakken labarin daga baya:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp