A ranar Laraba Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da kudirin Gwamna Ahmed Aliyu na kafa rundunar samar da zaman lafiya a jihar.
Wannan amincewar ta biyo bayan nazarin rahoton da kwamitocin majalisar hadin guiwa kan ayyuka na musamman da harkokin tsaro da shari’a da kwamitin kare hakkin bil’adama suka yi.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Halaka Mutum 1, Tare Da Sace Mutane 6 A Sokoto
- Ana Fargabar Sakamakon Hukuncin Zaben Gwamnan Sokoto Da Kotu Za Ta Yanke Yau Litinin
Shugaban Kwamitin, Alhaji Nasiru Adamu (PDP-Goronyo), ya ruwaito cewa, an binciki kudurin dokar, wanda ya samar da shawarwari 28.
“Wadannan shawarwarin sun hada da sake fasalin dokar zuwa, ‘Kudirin dokar kafa hukumar tsaro ta al’ummar jihar Sakkwato, da samar da zaman lafiya da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu, da kuma gaggauta daukar matakan gaggawa,” in ji shi. .
Adamu ya kara da cewa akwai bukatar a samar da sabon sashe dangane da adadin jami’an da ke aiki da kuma gyara kura-kuran rubutu, fasaha da rubutawa daga sashin kula da shari’a.
Shugaban majalisar Alhaji Tukur Bala ya gabatar da rahoton domin tantancewa kuma ‘yan majalisar sun amince da bukatar ta hanyar kada kuri’a.