A yau Lahadi majalisar gudanarwar kasar Sin ta nada manyan jami’an da zasu jagoranci gwamnati na 6 na yankin musamman na Hong Kong (HKSAR) na kasar, wanda yayi daidai da amincewar sabon kantoman yankin John Lee, da kuma bisa dacewa da tsarin muhimman dokoki yankin HKSAR.
Lee, wanda ya lashe zaben shugabancin yankin, wanda aka gudanar a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata, zai kama aiki daga ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2022 da muke ciki.
Sabbin jami’an da aka zaba zasu fara aiki ne a rana guda tare da sabon shugaban na yankin HKSAR.(Ahmad)