A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Sokoto ta gabatar da kudirin neman gwamnatin jihar da ta faɗaɗa shirinta na ciyar da abinci a watan Ramadan zuwa kananan hukumomi 23 na jihar baki daya maimakon ta takaita a babban birnin jihar.
Alhaji Bashar Isah (PDP-Tambuwal ta Gabas) ne ya gabatar da kudirin, sannan Alhaji Kabiru Dauda (APC-Gada ta Gabas) ya goyi bayansa.
- Tinubu Ya Tafi Kasar Qatar Don Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwanci
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Zartar Da Dokar Karya Farashin Magunguna
Ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa, marasa karfi a fadin jihar sun sami damar cin abinci mai inganci a cikin watan azumin Ramadan.
Da yake gabatar da kudirin, Isah, ya bayyana al’adar gwamnatin jihar na samar da kayan abinci a babban birnin kasar a cikin watan Ramadan kawai, sannan ya bayar da shawarar faɗaɗa wannan shirin zuwa sassan jihar baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp