Majalisar Dattawan ta bayyana Sanata Aniekan Bassey a matsayin sabon shugaban kwamitin kula da ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da kuma ƙungiyoyin fararen hula, a matsayin wanda zai maye gurbin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke kan dakatarwa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da naɗin sabon shugaban kwamitin yayin zaman majalisar na yau Alhamis. Wannan sauyi ya biyo bayan canjin da aka fara tun a watan Fabrairu, inda aka mayar da Akpoti-Uduaghan daga kwamitin kula da abubuwan da ake samarwa a cikin gida zuwa da NGOs.
- Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
- Lauyoyin Majalisar Dattawa Sun Ƙaryata Natasha Kan Cewa Kotu Ta Ce Ta Koma Bakin Aiki
Sanata Bassey na wakiltar mazaɓar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas, kuma ba a bayyana dalilin cire Akpoti-Uduaghan daga muƙamin ba a hukumance. Sai dai ana danganta hakan da dakatarwar da har yanzu ba a warware ba, duk da cewa wata kotu ta bayar da umarnin a dawo da ita bakin aikinta a watan Mayu.
Koda yake kotu ta bayyana dakatarwar a matsayin “tsanantawa da rashin bin doka,” lauyan majalisar dattawa Paul Daudu (SAN) ya bayyana a cikin wata shawara cewa hukuncin kotun bai bayar da umarnin tilas ba na mayar da ita cikin gaggawa. Akpoti-Uduaghan dai ta ce tana jiran kwafin hukuncin na doka kafin ta koma majalisa.
Ta ce ci gaba da hana ta dawowa majalisa ba wai kawai keta haƙƙinta ne ba, har ma da tauye wakilci ga mata da yara a Nijeriya, ganin cewa daga cikin mata takwas da suka yi sanata a baya yanzu uku kacal ne suka rage.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp