Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa Majalisar Tarayya na ƙara samun koma baya, tana rikitowa zuwa matsayin damusar takarda, saɓanin irin ƙarfin da ya kamata ta kasance da shi a tsarin dimokuraɗiyya.
A cikin wani jawabi da ya shirya gabatarwa yayin zaman haɗin gwuiwar Majalisar tarayya domin murnar ranar Dimokuraɗiyya, Saraki ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakai na gaggawa da nufin ƙarfafa wannan muhimmin ginshiƙin dimokuraɗiyya. Koda yake ba a samu damar karanta jawabin ba saboda gajeren lokaci, ya wallafa cikakken saƙon a shafinsa na X.
- Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?
- Bukola Saraki Ya Tallafawa Al’ummar Mokwa Da Gudunmawar Kuɗi
Saraki ya jaddada cewa babban nauyin da ke kan wannan zamani shi ne kula da ɗorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya, amma hakan ba zai yiwu ba sai da ƙarfi da cikakken ‘yancin Majalisar tarayya. Ya ce, “Bari in faɗi gaskiya: sai mun yarda da kanmu cewa ƙarfin Majalisar tarayya na raguwa sosai daga yadda majalisa mai ƙarfi da tasiri ya kamata ta kasance.”
Ya buƙaci ‘yan majalisar da su tabbatar da adalci ga waɗanda suka yi gwagwarmaya don kawo wannan dimokuraɗiyya da kuma al’umman Nijeriya da za su zo nan gaba. Ya ce yanzu alamu na nuna muna samun koma baya, kuma matsalar ba ta ta’allaƙa da majalisa kaɗai ba.
A cewarsa, “Ɓangaren zartaswa da na shari’a na daga cikin waɗanda ke ƙara raunana Majalisar Tarayya. Daga tsoma baki a zaɓin shugabanni, da rashin fahimtar rawar da majalisa ke takawa wajen sa ido, da kuma ɗaukar rashin amincewarta a wasu lokuta a matsayin kiyayya.”
Ya kuma tuna irin muhimmiyar rawar da Majalisar tarayya ta taka a lokuta masu sarƙaƙiya a tarihin Nijeriya, ciki har da daƙile shirin ƙara wa’adi na uku da kuma kafa “Dokar Bukata” lokacin rasuwar tsohon shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp