A ranar Litinin da ta gabata ne, wata gawa da aka gano a harabar majalisar tarayya ta bai wa mahukuntan majalisar matuƙar mamaki.
Hakan na zuwa ne, a daidai lokacin da ƴansanda suka ƙaddamar da wasu na’urori, domin ƙoƙarin bankaɗo gawar mamacin da aka samu a cikin motarsa ƙirar ‘Peugeot 406’, mai ɗauke lamba kamar haka; BWR- 577 BF.
- Shettima Ya Yaba Wa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Ƙwarewa Ta Jihar Kaduna
- Gwamna Yusuf Zai Kaddamar Da Majalisar Shurah Ta Jihar Kano
Sun bayyana matuƙar mamakinsu da afkuwar lamarin, yayin da wakilinmu a majalisar dattawa ya tuntuɓi Daraktan Yaɗa Labarai, Mr Bullah Audu Bi – Allah.
“Kawai jin labarin na yi, abin kuma ya yi matuƙar ba ni mamaki tare da furgici,” in ji shi. Har ila yau, kamar yadda ya bayyana a rahoton nasa, mamacinbama’aikacinmajalisar dokoki ta ƙasa ba ne.
Kazalika kuma, rundunar ƴansanda a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya fitar a ranar Litinin ta bayyana cewa; ana ci gaba da gudanar da bincike, domin gano sunan mamacin.
ya kuma isa wurin tare da gano gawar mamacin a cikin wata mota ƙirar ‘Peugeot 406’, ɗauke da lamba kamar haka; BWR-577 BF.
“Ba tare da ɓata wani lokaci ba, aka kai gawar zuwa babban asibitin Asokoro, inda likitoci sukatabbatardacewa; hargawar ta fara ruɓewa. “Kwamishinan ƴansanda na babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan wannan al’amari da ya faru tare da bayar umarnin ƙara ƙaimi wajen gano ko wane ne mamacin.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp