Majalisar wakilai a zamanta na ranar Alhamis ta dauki matakin dakatar da shirin karin kudin wutar lantarki da Kamfanin Rarraba wutar (DISCOS) ke shirin yi.
Don haka, majalisar ta bukaci hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NERC da kada ta amince da wata takardar bukatar karin kudin wutar lantarki a Nijeriya.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Hon. Aliyu Sani Madaki daga Kano, wanda ya bayyana cewa, kwanankin baya, kamfanin DISCOS ya sanar da a abokan huldarsa game da shirin karin kudin wutar lantarki dubi da yanayin harajin shekara-shekara (MYTO).
Madaki, ya yi nuni da cewa, takardar da DISCOS ta fitar ta bayyana cewa, daga ranar 1 ga watan Yulin 2023, za a sake yin nazari a kan farashin wutar lantarki.
Dan majalisar ya ce a karkashin tsarin MYTO, 2022, harajin yana kan sikelin Naira N441 kan duk dalar Amurka daya ( N441/$1), amma ana sa ran zai iya kaiwa zuwa kusan Naira N750 akan duk dalar Amurka daya (N750/$1 ) bayan kammala nazarin kamfanin.