Majalisar Wakilai ta bukaci hukumomin tsaro su tura jami’an tsaro cikin gaggawa zuwa mazaɓar tarayya ta Kebbe/Tambuwal da ke jihar Sakkwato domin shawo kan karuwar ayyukan ta’addanci a yankin.
Matakin majalisar ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da Honarabul Abdussamad Dasuki da ke wakiltar mazabar ya gabatar a zaman majalisar a ranar Talata kan yadda ‘yan ta’adda ke jefa firgici a tsakanin al’ummomin yankin
An samu yawaitar hare- haren ayyukan ta’addanci a Kebbe/Tambuwal, kisan al’umma da garkuwa da mutane da tarwatsa garuruwa da dama. A kwanan nan al’ummar yankin sun bukaci gwamnati ta ba su damar mallakar makamai domin kare kai.
Al’ummar yankin sun bayyana cewar matsalar tsaron ta gurgunta tattalin arzikin yankin musamman ayyukan noma wanda ya sa ɗaruruwan mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira a Sakkwato da makwabtan jihohi.
Dasuki ya bayyana cewar a ranar 12 ga Augusta 2025, ‘yan ta’adda sun shiga mazaɓar Fakku a karamar hukumar Kebbe tare da kashe mutane biyar da garkuwa da mutane 28 da satar shanu 37.
“Haka ma a ranar 15 ga Agusta, ‘yan bindigar sun kai farmaki mazaɓar Sangi tare da tilastawa jama’a neman mafaka a Kuchi da Koko a jihar Kebbi. Bugu da kari a ranar 18 ga Agusta ‘yan ta’adda sun afkawa mazabar Ungushi tare da kisan mutane biyu da garkuwa da mutane bakwai tare da asarar dabbobi.”
Dasuki ya kuma bayyana cewar, mazaɓun Jabo a karamar hukumar Tambuwal da Tambuwal/Shimfiri suna fuskantar kalubalen tsaro da ke bukatar agajin gaggawa.
Dan majalisar ya bayyana halin kuncin da al’ummar yankin ke ciki, ya ce munanan hare- haren sun tarwatsa kwanciyar hankalin al’umma, jama’a sun kauracewa garuruwa, haka ma yara sun daina zuwa makaranta, a yayin da manoma sun dakatar da zuwa gona a bisa ga tsoron ta’addancin.
A bisa ga amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci rundunar sojin Nijeriya da rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tura jami’an tsaro domin karfafa kai hare- hare a yankin Kuchi a karamar hukumar Kebbe da yankunan karamar hukumar Tambuwal domin kare rayuka, dukiyoyi da gonaki.