Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan kayyade kudaden da mutane za su ke cirewa.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa, Majalisar Wakilai ta soki sabuwar manufar da babban bankin Nijeriya (CBN), ya bullo da shi, wanda ya sanya iyaka wajen fitar da kudade a bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.
Saboda haka majalisar ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, da ya zo ya bayyana wa majalisar manufofin tsari.
A ranar yammacin Alhamis ne zai bayyana gaban majalisar.
Hakan ya samo asali ne a kan kudirin gaggawa da Aliyu Magaji, ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis.
‘Yan majalisar da dama sun yi gargadin cewa manufar za ta yi mummunar illa ga ‘yan kasuwa da ‘yan Nijeriya da ba su da damar yin amfani da tsarin banki.
Shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu, ya ce manufar za ta binciki laifuka domin a yanzu za a binciki kudaden ta hanyar banki.
Ya ce duk da kalubalen tsarin, kasar nan za ta fi amfana da shi.