An tashi barambaran a Majalisar Wakilai lokacin da ake gabatar da bukatar sahale wa shugaba Bola Tinubu damar karbar aron kudi daga babban bankin Nijeriya (CBN).
‘Yan majalisa na banagaren adawa sun fice daga zauren cikin bacin rai saboda a cewarsu majalisar ba ta saurari ra’ayinsu ba kan batun.
- Zanga-zanga: Shugaban Majalisa Ya Roki ‘Yan Nijeriya Su Kara Ba Wa Tinubu Lokaci
- An Kaddamar Da Shirin “Sabon Zamani Da Sabon Fim” Karo Na 2
Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu ne, ya gabatar da bukatar da ta nemi kara adadin kudin da CBN zai iya bai wa gwamnatin tarayya bashi da ake kira ‘Ways and Means’ ba tare da sahalewar majalisun dokoki ba.
Kudirin ya nemi a mayar da bashin kashi 10 cikin 100 maimakon biyar da doka ta tanada a yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp