Taron majalisar zartarwa na Shugabannin Ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) ya maida hankali kan batun matsalar tsaro da ya addabi al’ummar Nijeriya.
Taron ALGON karo na 48 ya gudana ne a garin Lafia, Gidan gwamnatin jihar Nasarawa wanda yafi maida hankali kan matsalar tsaro.
- Gyare-Gyaren Da Sin Ke Yi Zai Samar Da Karin Moriyar Bude Kofa Ga Duniya
- Kalaman Batanci Akan Matatatar Man Fetur Ta Dangote Barazana Ce Ga Nijeriya Da Afirka – Masani
Taron ya samu halarta manyan Shugabannin Ƙananan Hukumomi daga jihohi 36 na tarayyar Nijeriya, inda taron ya janyo hankalin mahalartan kan yadda za su gudanar da ayyukansu.
Shugabannin sun bukaci maido da zaman lafiya a yankunansu domin ci gaban harkokin noma, inda suka kara da cewa, zaman lafiya shi ne kan gaba, da zai janyo kowane mataki na ci gaba.
Tunda farko taron, ya godewa Gwamnan jihar Nasarawa Engr. Abdullahi Sule saboda gudummawar da ya baiwa kungiyar ta yadda taron zai gudana.
Sun kara da cewa, Gwamnan ya taya su murna saboda nasarar da suka samu a kotun koli.
Taron ya godewa Sarkin Lafia, mai shari’a Sidi Muhammad Bage saboda kyakkyawar tarba da ya yi musu a lokacin da suka ziyarci fadarshi.