Shekara guda ke nan da aukuwar rikici tsakanin Ukraine da Rasha, rikicin da kawo yanzu ya haddasa miliyoyin ‘yan gudun hijira, baya ga kuma mummunan tasirin da ya haifar ta fannonin samar da abinci da makamashi da ma farfadowar tattalin arzikin duniya.
Da Rasha da Ukraine da ma sauran kasashen Turai da ke kusa da fagen yakin, har ma da sauran kasashen duniya da suka hada da na Afirka, duk sun dandana kudar rikicin, akasin yadda Amurka ke cin moriyar siyasa da mummunar riba ta hanyar samar da makamai.
Alkaluman da majalisar gudanarwar kasar Amurka ta samar sun nuna cewa, a shekarar kudi ta 2022, yawan makaman da kasar Amurka ta sayar zuwa ketare ya karu da kimanin 50% bisa na shekarar 2021, kuma daya daga cikin dalilan haka shi ne barkewar rikici a tsakanin Ukraine da Rasha.
Kwanan baya, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kai ziyara ta ba zata Ukraine, inda ya sanar da karin gudummawar soja da za su kai dala miliyan 500 da za ta samar wa Ukraine, kuma hakan na zuwa ne kasa da wata guda, bayan wata gudummawar soja da ta sanar a farkon wannan wata. Labarin da kamfanin dillancin labarai na AP ya bayar ya shaida cewa, gaba dayan gudummawar soja da Amurka ta samar wa Ukraine ya zarce dala biliyan 50.
A shekarar da ta gabata ce rikici ya barke tsakanin Ukraine da Rasha, sakamakon yadda Amurka ta rura wutar rikicin, yanzu haka, shugaban Amurka ya kara rura wutar a ziyararsa, a maimakon ya taimaka ga tabbatar da zaman lafiya.
A yayin da ake cika shekara guda da aukuwar rikicin, ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayar da wata takarda a jiya, inda daga wasu fannoni 12 ta nanata matsayinta na daidaita matsalar Ukraine a siyasance, a cewarta, yin shawarwari shi ne hanya daya tilo wajen daidaita rikicin.
Idan mun waiwayi baya, za mu ga cewa, kasar Sin ta sha neman tabbatar da sulhu a tsakanin kasashen biyu. Ko da a kwanakin baya ma, ta yi shawarwari a kai tsaye da Ukraine da ma Rasha bi da bi, inda take kokarin neman sassauta mummunan yanayin da ake ciki.
A cikin shekarar da ta gabata, kasar Sin ba ta taba tsayawa tana kallon rikicin ba, ballantana ta rura wutar rikicin, kuma hakan ya faru ne sakamakon irin ra’ayoyi na “zama lafiya da juna da martaba bambance-bambance” da “zama lafiya da kasa da kasa” da “kawar da yake-yake a duniya” da ke cikin al’adun gargajiya na tsawon tarihi na shekaru sama da 5000 na kasar Sin, ra’ayoyin da a zamanin yau aka bayyana su a cikin shawarar kiyaye tsaron duniya da kasar ta gabatar, wato a rika yin shawarwari a maimakon yin fito na fito, kuma a yi hadin gwiwa a maimakon kulla kawance, da ma cin moriyar juna a maimakon cin nasara daga faduwar wani bangare.
Matsalar Ukraine ta kara nunawa al’umma cewa, tsaro ba hakkin musamman na wasu kasashe ba ne, kuma bai kamata a lalata tsaron wata kasa don tabbatar da na wata ba, kuma habaka kawancen soja ba zai haifar da kome ba, illa ya lalata tsaron shiyya.
Makomar dan Adam daya ce. Tabbatar da dauwamammen ci gaban duniya, ta yadda al’ummar kowace kasa za ta iya rayuwa cikin kwanciyar hankali da walwala, burinmu ne na bai daya. Duk wahalar da za a fuskanta, ya zama dole a daidaita matsalar Ukraine a siyasance. Aikin da muka sanya a gaba shi ne a tabbatar da tsagaita bude wuta a tsakanin kasashen biyu cikin gaggawa, kuma makamai ba za su tabbatar da zaman lafiya ba. (Mai zane:Mustapha Bulama)