Duk da yawan ikirarin da gwamnatin jihar Yobe ta sha yi wajen inganta harkokin ilimi, kafa kwamitin sake farfado da fannin, wakilinmu ya gano wata makarantar firamare a kauyen Ngelshengele da ke karamar hukumar Fune a jihar; mai malamai biyu kacal tare da adadin dalibai 544 a ajujuwan makarantar.
LEADERSHIP Hausa ta jiyo ta bakin shugaban makarantar (Headmaster) Malam Sa’id Wakil, inda ya koka dangane da rashin malamai a makarantar, kana kuma al’amarin da ya ce yana daya daga cikin manyan kalubalen da Firamare ta Ngelshengele ke fuskanta. Inda ya ce malamai biyu ne kawai a makarantar.
“Akwai wani malami daya wanda aka turo shi zuwa wannan makarantar, amma mun gano cewa dalibi ne daga Gashuwa. Sannan a gaskiya ban ma san shi ba, amma ko shakka babu zuwan sa zai taimaka.” inji shi.
Malam Sa’id ya ce, “Baya ga rashin malamai, kusan dukkan ajujuwan wannan makaranta na bukatar gyara. Kamar yadda kuke gani, duk sun lalace.”
Bugu da kari kuma, ya ce duk da an gyara wasu azuzuwan ne ta tallafin bankin duniya da kwamitin kula da makarantu (SBMC). Ya kara da cewa, kimanin N500,000 ne aka tara domin gyara wasu azuzuwan da daliban ke daukar darasi a halin yanzu.
A hannu guda kuma, da yake ci gaba da tsokaci kan kalubalen da Firamaren ke fuskanta, shugaban makarantar ya ce a lokacin damina, da zarar sun ga alamar hadari ya taso, sai su tura daliban gida, su kwashe kayan karatu; kujeru da makamantan su zuwa gidan Hakimin kauye domin kaucewa faruwar hatsari ga daliban daga ruwan sama da iska su halaka su.
Ya kara da cewa, wadannan matsalolin sune suke tilastawa yara da dama barin makaranta a kauyukan, al’amarin da ya katangance yaran daga yancin samun karatu.
A nashi bangaren, Kwamishina a Ma’aikatar Ilimi a matakin farko a jihar Yobe, Dokta Muhammad Sani Idrissa, ya ce “To, gwamnatinmu ta gaji halin kuncin da fannin ilimi ke ciki, musamman yanayin da wasu makarantun ke ciki. Mun fahimci cewa akalla makarantun firamare da sakandare 1,300 ne ke bukatar gyara. Amma cikin kankanin lokaci mun gyara akalla guda 300 kuma muna fatan nan gaba kadan makarantu 1000 za su kasance a cikin ayyukanmu na gyara da muke yi, kuma Makarantar Firamare ta Ngelshengele za ta kasance a cikinsu,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp