Tsohon dan wasan gaban Manchester United Wayne Rooney wanda kungiyar kwallon kafa ta Birmingham City wadda ke buga gasar ‘yan dagaji ta Kasar Ingila ta kora bayan rashin tabuka abin a zo a gani.
Ya bayyana cewar kungiyar ta Birmingham ba ta bashi lokacin da ya kamata domin dawo da kungiyar cikin hayyacinta ba, inda ya bayyana cewa sati 13 da aka bashi ya yi kadan.
Kungiyar Birmingham City ta kori kocinta Wayne Rooney bayan ya shafe kwanaki 83 yana jan ragamar kungiyar a gasar Championship.
An nada Rooney mai shekaru 38 a ranar 11 ga Oktoba, biyo bayan yanke shawara mai cike da cece-kuce na korar tsohon kocin kungiyar John Eustace a lokacin da take matsayi na shida a kan teburi.
Tun daga wannan lokacin sun koma mataki na 20, rashin nasarar da suka yi a ranar Litinin da ci 3-0 a hannun Leeds shi ne rashin nasara na 9 a wasanni 15 da ya jagorancesu.
Rooney ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa kwallon kafa wata aba ce wadda ake bukatar sakamako mai kyau,amma na fahimci cewar ba su samu wannan sakamakon da suke bukata ba.
Ina so in gode wa mamallakan kungiyar Tom Wagner da Tom Brady saboda damar gudanar da Birmingham City da kuma goyon bayan da suka ba ni a cikin gajeren lokaci na a kulob din in ji shi.
Duk da haka, lokaci shi ne abu mafi daraja da mai horarwa yake bukata kuma ban yi tunanin makonni 13 sun isa domin in kawo canje canjen da ake bukata ba.
Rooney ya bayyana cewar yana bukatar dan wani lokaci kafin ya shawo kan wannan koma baya da kungiyar ke fuskanta.
Na tsunduma cikin harkar kwallon kafa, a matsayina na dan wasa ko kuma mai horarwa tun ina dan shekara 16.
Amma yanzu, na yi shirin daukar lokaci tare da iyalina yayin da nake jiran samun dama ta gaba domin cigaba da aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp