Daya daga cikin malaman da ke jagorantar wa’azozi da harkokin addinin Musulunci a yankin Karamar Hukumar Kagarko, Malam Muhammad Rabi’u Aminu da ke Unguwar Masukwani Jere, ya zama sabon babban limamin Masarautar Jere.
Wannan ya biyo bayan nada shi da mai martaba Sarkin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya ya yi tare da mataimakansa guda biyu, limami na biyu, Malam Abubakar Idris Abubakar, da limami na uku Malam Is’hak Ibrahim Usman, a ranar Juma’a 10 ga Nuwambar 2023.
- Sakamakon Taron Kasashen Musulmi Da Larabawa: Saudiyya Da Nijeriya Za Su Jagoranci ‘Yantar Da Falasdin
- Sarkin Musulmi Ga Malamai: Ku Rika Shawartar Masu Mulki Kan Shugabanci Nagari
Da yake jawabi jim kadan bayan nadin, sabon babban limamin, Malam Muhammad Rabi’u, ya fara da cewa, “Farko muna godiya ga mai martaba Sarkin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya kuma tare da du’ai, Allah ya saka masa da alkhairi, da cikin jama’a ya zabe mu, mu zama mu ne jagorori na limancin wannan gari. Muna fata Allah ya kara masa lafiya. Sannan muna masa ta’aziyyar babban limaminmu da muka rasa, Allah ya gafarta masa, Allah ya sa ya huta, Allah ya sa aljanna ce makomarsa.
“Kuma daga ciki muna godiya ga majalisar mai martaba Sarkin Jere, bisa gudunmawar da suka bayar don su ga cewa an zauna lafiya, an hada kai. Muna musu fatan alkhairi, da fatan Allah ya saka musu da alkhairi. Sannan ina tabbatar muku da cewa, ni da sauran limamai wadannan muna zaune lafiya, kanmu ya hadu. Kuma su malamaina ne, Allah ya saka musu da alkhairi.
“Daga cikin majalisar mai martaba Sarkin Jere akwai wani shiri da suka so su yi na hadin kan mutanen garin nan amma bai yiwu ba kuma da aka yi wannan tsarin na yanzu ba su ki ba, muna fatan Allah ya tabbatar da niyyarsu, Allah ya zaunar da mu lafiya ya saka musu da alkhairi.” In ji shi.
Malam Muhammad Rabi’u, ya yi kira ga sauran malamai su rika gyara musu idan sun ga kuskure cikin shugabancin harkokin addinin yankin da aka dora musu, yana mai cewa, “Duk abin da za mu yi na kuskure malamai su kira mu su gaya mana. Alhamdu lillah, daya daga cikin malamanu da ke irin wannan shi ne Malam Tanimu. Idan ya ji ka yi kuskure, zai kira ka a waje ya ce ina so zan yi maka gyara amma sai na zo, nakan ce a’a, ni ne zan zo, ba sau daya ba, ba sau biyu ba yana mana irin wannan gyara, Allah ya saka masa da alkhairi. A madadin wadannan limamai muna ma jama’ar musulmi godiya da suka ba mu goyon baya da hadin kai da fatan zaman lafiya. Allah ya zaunar da mu lafiya.” Ya bayyana.
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya, ya yi kira ga sabon babban limamin da sauran mataimakansa su zama masu koyar da mutane a aikace ba da wa’azi da baki ba kawai, kana ya bukaci daukacin al’ummar masarautar su zama masu kyautata wa iyali da zaman lafiya.
“Addinin Musulunci da shi Allah zai mana hisabi gobe kiyama. Wanda ya ci jarrabawa ya tsira, wanda ya samu akasin haka kuma a uzu billahi. Ina kira ga limaman da muka nada yau su zama masu aikata abubuwan da suke wa’azi a kai, daga aiki ake so a rika koyarwa.Kuma ina kira ga daukacin al’ummmar Jere su zama musulmi na kirki da lyautata wa iyali da zaman lafiya. Kowa ya tsaya kan gaskiya, ban da dabi’u marasa kyau. Da ire-iren wadannan Allah zai dube mu da idon rahama ya sa mu a gidan Aljanna.” Ya bayyana.