Malamai da sauran mahalatta taron kaddamar da littafi da faifan CD na wakokin bege na ma’aikin Allah, sun yaba wa Sarkin Sha’iran Kano, Malam Ibrahim Yusuf Kaulahi kan hidima da ya yi wa ma’aikin Allah na yabansa da Ahlinsa da kuma Sahabbansa.
Sarkin Sha’iran Kano wanda ya shafe sama da shekaru 40 yana yabon ma’aiki, malaman sun bayyana cewa akwai bukatar al’ummar Musulmai su yi koyi da halayansa wajen yi wa ma’aiki hidima.
Taron kaddamar da lattafi da faifen CD ya gudana ne a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Asabar da ta gabata.
Daga cikin malaman da suka yaba wa sarkin sha’iran Kano akwai Shugaban Majalissar Malamai na Arewa, Sheikh Ibrahim Khalil wanda ya ce yin haka abun ne da yake nuna nagarta, domin haka akwai bukatar matasa su yi amfani da basirarsu wajen yin aiki da zai taimaki addini tare da yada alkairi a tsakanin al’umma.
Shi kuma masanin fannin ilimin addinin musulunci da kuma ilimin sannin tsirrai, ganyayyaki, sauyoyi a ilimi addinin musulunci, Dakta Saluhunnoor ya ce zuwansa wannan taro zabi ne na Allah, amma dai abun da ya shafi Manzon Allah ba ya wasa a cikinsa, kuma wajibi ne musulmi ya ba da gudummawarsa daidai yadda zai iya.
Ya kuma nuna godiyasa ga Allah da wannan taro na kaddamar da littafi da faifen CD na ma’aiki da Sarkin Sha’iran Kano ya wallafa.
Tun da farko a jawabinsa, Sarkin Sha’iran Kano, Mallam Ibrahim Yusuf Kaulahi ya ce ya shafe shekara sama 40 yana wannan wake na ma’aikin Allah.