Malaman Jami’ar Taraba (TSU) da suka fara yajin aiki sun bayar da sharuɗɗan da za su sa su dawo aji.
Shugaban ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Taraba, Comr. Joshua Mbave, ya bayyana waɗannan sharuɗɗan yayin ganawa da LEADERSHIP a Jalingo, babban birnin jihar Taraba a yau Jumma’a.
- Babu Shirin Rushe Babban Masallacin Jalingo – Gwamnatin Taraba
- ‘Yan Bindiga 3 Da Mai Yin Safarar Makamai Sun Shiga Hannu A Taraba
Malaman sun zargi gwamnatin jihar da rashin haɗa su cikin sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka fara biya a watan Nuwamba 2024.
Haka kuma sun lissafa wasu matsalolin da suka haɗa da rashin biyan alawus ɗin malamai da haƙƙoƙin fansho, da rashin majalisar jami’a da zata ɗauki mataki kan al’amuran ci gaba, da kuma rushewar tattaunawar kan buƙatunsu.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai da sadarwa, Hon. Emmanuel Bello, ya buƙaci malaman su dawo aji domin a ci gaba da tattaunawa game da buƙatunsu. Sai dai, Mbave ya tsaya tsayin daka, yana mai cewa ba zai yarda a koma aji ba har sai an cika dukkanin buƙatunsu.