Bayan barazanar da Nasir El-Rufai y yi cewa sai ya sallami duk wani malamin Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da ya ci gaba da yin yajin aikin ASUU, malaman sun dawo aiki gadan-gadan a jiya Litinin.
Rahotanni sun ce dalibai sun yi ta tururuwa zuwa jami’ar domin ci gaba da karatu.
- An Yi Wa Sama Da Mutum 130 Gwajin Cutar Hanta Kyauta A Kano
- Mayakan Taliban Sun Yi Arangama Da Masu Gadin Iyakar Iran
Sai dai kuma ba karatu a ka yi ba a wannan rana, inda daliban sun ci gaba da jarabawa ne wacce suna tsaya da yi kafin tafiya yajin aikin.
Dalibai sun garzaya dakunan karatu duk sun zauna domin fara rubuta jarabawa.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Nasir El-Rufai, ya yi barazanar cewa duk malamin da ya shiga yajin aikin malaman jami’o’i zai fuskanci hukuncin gwamnati.
”Na rantse duk malamin da ya shiga yajin aiki zan kore shi daga aiki. Domin jami’ar gwamnatin jiha ce KASU ba ta gwamnatin tarayya ba. Mu ne muke biyansu albashi saboda haka dole su koma aiki. Wanda kuma yaki zai gani a asusunsa.
”Sannan kuma za mu duba duk wanda ya karbi albashinmu kuma ya yi yajin aiki a baya zai biya mu idan muka gano haka.”
Har yanzu malaman Jami’o’i na ci gaba da yajin aikin a fadin kasar nan.
Sun fara yajin aiki tun daga watan Faburairu har yanzu.
Yajin aikin da ASUU ke yi ya janyo kungiyoyi da dama sun shiga zanga-zangar goyon bayansu don kawl karshen yajin aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp