Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa ta cika hannunta da wani malamin makarantar tsangaya kan zargin aikata luwaɗi da ɗaliban makarantarsa 13 a ƙaramar hukumar Gwaram.
Wanda ake zargin mai suna Yusufa Yunusa, dan kimanin shekaru 23 wanda ya kasance mai koyar da yaran karatun Alkur’ani, an kama shi ne bayan da aka samu labarin yana tilasta wa daliban yin lalata da su a wurare daban-daban.
- Sabon Tsarin Karatun Sakandare Zai Fito A Watan Satumba – Minista
- Kwamitin Kolin JKS Ya Amince Da Kudurin Kara Zurfafa Sauye-sauye Daga Dukkanin Fannoni
Yayin holen wanda ake zargin ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Dutse, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP AT Abdullahi, ya ce wanda ake zargin ya kan ja ɗaliban wurare daban-daban tare da tilasta musu wasa da al’aurarsa, sannan ya sanya su wasu abubuwan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp