Wani rukuni na ƙungiyar matasan jam’iyyar APC (APC-YLA) sun yi zaman dirshan a shalƙwatar hukumar EFCC a Abuja inda suka yi kira da a sake buɗe binciken zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa ministan tsaron ƙasa Bello Matawalle.
Shugaban ƙungiyar Muhammad Isah ya gabatar da wasiƙar koke ga hannun daraktan tsaron EFCC Idowu Adedeji, inda ya buƙaci hukumar ta ci gaba da binciken don tabbatar da gaskiya da adalci a yaƙi da cin hanci.
- Zamfara: Yadda Zargin Juna Da Hannu A Ta’addanci Ya Yi Kamari Tsakanin Dauda Da Matawalle
- Ziyarci Jihar Zamfara
An gabatar da wasu koke-koke a shalƙwatar EFCC, ciki har da na ƙungiyar APC Akida Forum a ranar 3 ga Mayu 2024 da wani ƙarin koke a ranar 30 ga Satumba 2024, suna roƙon hukumar da ta ci gaba da binciken tsohon gwamnan jihar Zamfara.
“A ranar 18 ga Mayu 2023, EFCC ta sanar da cewa tana binciken Matawalle kan zargin cin hanci, ba da kwangiloli na ƙarya da kuma satar fiye da biliyan N70.
Kudin da aka samo a matsayin lamuni daga wani tsohon banki, wanda aka ce za a yi amfani da shi wajen aiwatar da ayyuka a jihar, an yi zargin cewa gwamnan ya sace ta hanyar wasu mutane da ‘yan kwangila waɗanda suka karɓi kuɗin amma ba su yi aikin ba,” in ji Isah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp