Man City Ta Lallasa Real Madrid Har Gida

Kungiyar Manchester City ta bi Real Madrid har gida ta ci ta da ci 2 da 1 a wasan farko na zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai., Wasan dai an buga a filin wasa na Real Madrid na Santigo Bernabeu.

Kungiyoyin biyu sun kammala minti 45 ba tare da kwallo ya shiga raga ba. Sai dai bayan da suka koma zagaye na biyu ne Francisco Alarcon Suarez ya ci wa Real kwallo. Daga baya City ta farke ta hannun Gabriel Jesus, sannan saura minti bakwai a tashi Kevin de Bruyne ya kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kafin karawar a Sipaniya, kungiyoyin sun fafata sau hudu a gasar ta Zakarun Turai, inda Real ta ci wasa biyu da canjaras biyu.

Exit mobile version