Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Christian Eriksen zai shafe akalla wata biyu yana jinya, bayan samun rauni a wasan kofin kalubale da suka buga da Reading ranar Asabar.
Sai dai kociyan kungiyar, Erik Ten Hag ya yi amanna cewa Manchester United na da ”yan wasa da za su iya cike gibin da Eriksen zai bari wanda hakan ya sa yake ganin ba shi da damuwa.
Ten Hag ya ce ranar karshe abu ne mai wahala a iya cike madadin dan wasa kuma a matsayinka na mai koyarwa ba za ka dauki mataki ba bagatatan saboda rauni, to amma kuma suna da ‘yan wasa a tsakiya kuma suna da kyau.
Dan wasan na Denmark ya buga wa Manchester United wasanni 31 a wannan kaka, bayan da ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara uku kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan da United take takama da su.
Kafin zuwan Eriksen Manchester United, ya yi kwallo a kungiyoyin Ajad da Tottenham da Inter Milan kafin ya tafi Brentford inda ya buga wasa a watanni shida kacal a kungiyar.
Watakila dan wasan tsakiyar ya iya kai wa har farkon watan Mayu kafin ya murmure, wato dab da a kare wannan kaka kenan kuma daman dan wasan kungiyar na tsakiya Donny Ban de Beek yana jiyya wanda ba zai dawo ba har sai bayan kammala wannan kaka.
Sai dai kuma Manchester United din ta karbi aron dan wasa Marcel Sabitzer daga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich wanda zai zauna har zuwa karshen wannan kakar.
Dan wasan tsakiyar na Austria mai shekaru 28 zai maye gurbin Christian Eriksen ne da ke fama da doguwar jinya da kuma Scott Mc Tominay da shima ya samu rauni a baya-bayan nan.
Sabitzer wanda Munich ta sayo daga RB Leipzig lokacin ya na matsayin kyaftin wasanni 54 ya dokawa kungiyar ta Bundesliga daga sayensa a 2021 zuwa yanzu kuma a jawabinsa bayan rattaba hannu kan yarejejeniyar zaman aron a tawagar Eric ten hag, Sabitzer ya ce amsa tayin zuwa Old Trafford matsayin aro ne saboda ya san cikakkiyar dama ce gareshi ya bayar da gudunmawarsa ga gungiyar.
A tsawon lokacin da ya shafe yana buga wasa a turai Sabitner ya buga wasanni sau 443 a filayen wasa ya yinda a bangare guda ya buga wa kasar sa wasanni 68 tare da cin kwallaye 12.