Manchester United sun kammala sayen ɗan wasan gaba na RB Leipzig, Benjamin Sesko, a kan kuɗi kimanin fam £73.7 miliyan. Sesko, ɗan ƙasar Slovenia mai shekaru 22, ya rattaba hannu kan kwangilar shekaru biyar tare da ƙungiyar. An biyan £66.3m kai tsaye, yayin da sauran kuɗin zai kasance a matsayin ƙari (add-ons).
Wannan shi ne sayen ɗan wasa na uku a ɓangaren gaba da United suka yi a wannan kakar, bayan sayen Matheus Cunha a kan fam £62.5m da Bryan Mbeumo a fam £65m, wanda £6m na ƙari ne. Dukansu an gabatar da su ga magoya bayan ƙungiyar kafin wasan wasannin shirin kakar a gida da Fiorentina ranar Asabar.
- Manchester United Da Everton Na Zawarcin Wilfred Ndidi
- Sin Ta Gabatar Da Korafi Da Babbar Murya Dangane Da Kalaman Jagoran Philippines
Ƙungiyoyin da suke neman Sesko sun haɗa da Newcastle United amma ya zaɓi tafiya ƙungiyar Ruben Amorim. United ta kammala kakar wasa ta baya a matsayi ta 15 a Premier League, yayin da Newcastle ta ƙare a matsayi na biyar kuma ta samu shiga gasar Champions League tare da lashe kofin EFL.
Sesko ya bayyana cewa ya na matukar jin daɗin damar da zai samu a Manchester United. Ya ce, “Tarihin Manchester United na da matuƙar muhimmanci, amma abin da ya fi ɗaukar hankalina shi ne makomar ƙungiyar. Daga lokacin da na iso, na ji yanayi mai kyau da kuma haɗin kai na dangi da ƙungiyar ta ƙirƙira.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp