• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

byRabilu Sanusi Bena and Sulaiman
4 months ago
Reijnders

Manchester City ta amince da yarjejeniya tare da AC Milan kan daukar dan wasan tsakiya na Holland Tijjani Reijnders, wannan cinikin zai kasance na farko da City za ta yi idan aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta bazara, in ji rahotanni.

Zakarun gasar Firimiya na shekarar 2024 Manchester City na shirin biyan Yuro miliyan 55 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 63 domin daukar dan wasan mai shekaru 26, wanda aka fahimci ya amince da kwantiragin shekaru biyar a Etihad, City na fatan kammala cinikin dan wasan na Netherlands kafin lokacin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa na FIFA da za a fara a ranar 14 ga watan Yuni.

  • Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027
  • Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

Reijnders ya koma AC Milan ne daga AZ Alkmaar a shekara ta 2023 kuma ya ci wa kungiyar ta Italiya kwallaye 15 a kakar wasanni ta shekarar 2024/2025, zuwan Rijnders zai kara yawan zabukan da Pep Guardiola ke da shi a tsakiya bayan tafiyar Kebin De Bruyne, ba a tsammanin tsohon dan wasan na Belgium zai taka leda a gasar cin kofin duniya, inda ake ganin zai iya komawa Napoli mai rike da kofin Seria A.

Mateo Kobacic ba zai samu damar buga gasar cin kofin Duniya na kungiyoyi ba sakamakon tiyatar da aka yi masa a Achilles (Gwuiwa), kungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta sha fama da rashin nasara a kakar wasa ta 2024/25, inda ta kare a matsayi na uku a gasar Firimiya kuma ta kasa lashe kofi a karon farko cikin shekaru takwas.

A makon da ya gabata shugaban City Khaldoon Al Mubarak ya yarda cewa kulob din ya kamata ya kashe kudade masu yawa a kasuwar musayar yan wasa gabanin fara kakar wasa ta badi domin karfafa kungiyar, City za su je gasar cin kofin duniya na kungiyoyi 32 da aka fadada a matsayin masu rike da kofin gasar bayan sun lashe gasar da aka yi a Saudiyya shekaru biyu da suka wuce.

LABARAI MASU NASABA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

Za su fara wasansu na farko da kungiyar Wydad Casablanca ta Morocco a Philadelphia ranar 18 ga watan Yuni, za a bude kasuwar musayar ‘yan wasa har zuwa ranar 10 ga watan Yuni domin karbar kungiyoyin da ke son sayen ‘yan wasa a gasar cin kofin duniya kafin a sake budewa a ranar 16 ga watan Yuni.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane
Wasanni

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni
Wasanni

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

October 6, 2025
Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar
Wasanni

Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar

October 6, 2025
Next Post
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version