Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila, ta amince dan wasan gabanta, Cristiano Ronaldo ya sauya sheka zuwa wata kungiyar.
Tun kafin fara kakar wasanni ta bana Ronaldo ya bayyana wa mahukunta kungiyar sha’awarsa na barin kungiyar.
- Matar Shugaban Kasar Amurka Ta Kamu Da COVID-19Â
- Takarar Musulmi 2: Magoyan Bayan APC Sun Yi Zanga-zanga A Legas, Sun Bukaci A Sauya Shettima
Sai da kungiyar a mabambamtan lokuta ta musanta cewar dan wasan na son barin kungiyar.
Kazalika, sabon kocin Manchester United, Erik Ten Hag shi ma ya ce sam babu abin da zai sa kungiyar ta raba gari sa fitaccen dan wasan gaban.
Ronaldo na son barin kungiyar sakamakon gaza samun gurbi a gasar zakarun turai, wanda hakan ya sa ta kare a gasar EUROPA.
An alakanta Ronaldo da kungiyoyi irin su Chelsea, Real Madrid, Bayern Munich, Barcelona, PSG da sauransu, amma har yanzu babu kungiyar da ta nuna sha’awar daukarsa.
Ronaldo na son ci gaba da buga gasar zakarun turai, musamman don ci gaba da kafa tarihi tare da yi wa kowane dan wasa fintinkau a gasar.
Sai dai ya zuwa yanzu ba a san kungiyar da za ta dauki dan wasan ba duba da irin zunzurutun miliyoyin kudi da ya ke dauka a matsayin albashi, ga kuma shekaru da suka fara cimma masa.