Kungiyar Manchester United ta kori dan wasa Mason Greenwood daga kungiyar bayan ta kammala bincike akan dan wasan.
An yi watsi da tuhumar da ake yi wa dan wasan mai shekaru 21, gami da yunƙurin fyade da kai hari a ranar 2 ga Fabrairu.
An sa ran cewa sanarwa za ta fito kafin fara gasar Premier da za su kara da Wolves a ranar Litinin amma aka jinkirta.
Yanzu dai dan wasan ba zai sake buga wa kungiyar wasa ba kuma lauyoyin kungiyar da na dan wasan zasu zauna domin soke kwangilar dan wasan.
Daman dai shawara game da makomar Greenwood a yanzu, ya rataya ne a wuyan babban jami’in zartarwar Æ™ungiyar Richard Arnold – kuma a halin yanzu ana kan matakin Æ™arshe.
Greenwood bai buga wasa a United ba tun lokacin da aka tuhume shi kuma bai shiga filin atisayen kungiyar na Carrington ba.