Sir Jim Ratcliffe zai biya fam biliyan 1.3 domin sayen kashi 25 cikin 100 na Manchester United bayan da babban dan kasuwan kasar Qatar Sheikh Jassim bin Hamad al Thani ya janye daga cinikin.
Tayin da Sheikh Jassim ya gabatar, wanda ya kai darajar United sama da fam biliyan 5 shi ne kawai tayin mallakar kashi 100 na kungiyar.
- Manchester United Zata Karbi Bakuncin Brentford A Filin Wasa Na Old Trafford
- Abin Da Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Leipzig Da Manchester City
Amma duk da hakan bai sa masu kungiyar Glazers Family wadanda suka mallaki United tun 2005 suka sallama ba,don haka Sheikh Jassim ya janye daga cinikin kungiyar.
Amma duk da haka Glazers sun amince su sayarda kashi 25 cikin 100 na kungiyar ga hamshakin dan kasuwar kasar Amurka Sir Jim Ractlife,inda ake sa ran kai karshen yarjejeniyar a wani zama da mahukuntan kungiyar zasu yi a wannan makon.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp