Rikicin filin gona ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu biyu a ƙaramar hukumar Gulani da ke Jihar Yobe. Lamarin ya faru ne a daren Asabar bayan ce-ce-ku-ce tsakanin mazauna ƙauyukan Zango da Azere, waɗanda ke tsakanin iyakokin Gujba da Gulani.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa shalƙwatar ƴansanda ta Bara ta samu kiran gaggawa daga shugaban ƙauyen Zango a ranar 9 ga Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda ya sanar da cewa wasu ƴan daba daga ƙauyen Azere sun kai mummunan farmaki kan manoma.
- Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama Ɗalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah
- Afam Osigwe Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Lauyoyi Ta Kasa
Wanda aka kashe sun haɗa da Sani Makeri, mai shekara 40, da Abdullahi Maicitta, mai shekara 35, dukkansu ƴan asalin Zango. An garzaya da waɗanda suka jikkata an kai su zuwa babban asibitin Damaturu domin samun kulawa.
SP Dungus ya ce rikicin ya samo asali ne tun bara lokacin damina, duk da ƙoƙarin hukumar ƴansanda wajen sulhu ta hanyar kwamitin daidaita iyakoki na Jiha. Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya la’anci harin tare da bayar da tabbacin cafke masu laifi, kana ya ja hankalin manoma su guji ɗaukar doka a hannu su kuma nemi sulhu ta hanyar hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp