Manoma a fadin kasar nan, sun shafe shekaru suna korafi kan matsalar rashin raba takin zamani da gwamnatin tarayya da kuma ta jihohi ke yi a kurarren lokaci.
Wannan Taki dai shi ne, babban sinadarin da manoma ke yin tunkaho da shi tare da dogaro kacokan a kansa, musamman don yin noman zamani.
Duba da wannan, LEADERSHI Hausa ta samu nasarar tattaunawa da wasu daga cikin fitattun manom a Jihar Kaduna tare kuma da wani masani a fannin tattalin arzikin kasa.
Alhaji Muhammad Adamu Makarfi, fitaccen manomi a Jihar Kaduna; sannan kuma Shugaban Kungiyar Manoman Masara a shiyyar Arewa Maso Yamma, ya bayyanawa rashin jin dadinsa na cewa; a yanzu ne ake cikin watan takwas, amma wai sai a yanzun ne a wasu yankuna namu; musamman na Arewacin wannan kasa ake yin rabon taki, don haka a cewar tasa tuni an riga an baro shiri tun a rani kenan.
Shugaban ya kara da cewa, muna bayar da shawara; musamman ga hukumomin da wannan abu ya shafa na rabon takin zamani da su daina bari lokaci yana yin nisa kafin su raba shi.
Alal misali kamar Masara, wata tana fara shigowa karshen watan Juli, musamman ga wadanda suka yi shuka tun cikin watan Afrilu, kenan idan an zuba mata takin zamani a cikin watan takwas, takin ba zai yi mata wani amfani ko tasiri mai yawan gaske ba.
Sai dai kawai ga ‘yan kalilan wadanda ba su yi shuka da wuri ba, su ne takin zai yi wa Masarar tasu tasiri a gonakinsu.
Amma a jihohi kamar irin su Kaduna, Kano, Katsina da sauran jihohin Arewa ta tsakiya, su kan fara yin shuka ne tun a cikin watan Afrilu.
Saboda haka, ya kamata idan za a fara rabon wannan taki, ka da a kuskura ya wuce karshen watan biyar, domin ganin cewa; takin da aka raba wa manoman, kwalliya ta biya kudin sabulu.
Har ila yau, muna fatan a duk lokacin da za a yi tsari ko aiwatar da rabon wannan taki; a tabbata an fara yin sa da wuri, idan so samu ne ma a ce an fara rabon tun a watan biyu, ta yadda ana shiga watan hudu; an fara raba wa manoman.
Ko shakka babu, wannan zai yi matukar taimaka wa manoma; musamman ganin cewa, su ma suna da irin nasu tsarin ko jadawali na yawan wuraren da suke son su noma, da kuma sauran irin abubuwan da suke so su shuka tare da yawan takin zamanin da kuma suke bukata.
A bangare guda kuma, sananniyar manomiya a Jihar Kaduna kuma Shugabar Gidauniyar Zulifat; Hajiya Aisha Abubakar, ita ma ta tofa nata albarkacin bakin; inda ta bayyana cewa, ”Kamar mu a nan Arewacin Nijeriya, akasarin manona sun fi yin noma da damina. Saboda haka, ya kamata a rika rabar da taki a kan lokaci, ba a kurararen lokaci ba; domin kuwa rabarwa a makare na haifar wa da manoma matsala.
“Amma ka ga wasu gwamnatocin jihohin, musamman a nan Kaduna; sai a cikin wannan wata na takwas sannan suka raba wa manoma takin. Don haka, idan muka dubi yadda yau a kasar nan ake cikin karancin abinci; rabar da takin cikin kurarren lokaci babu abin da zai kara haifarwa sai kara jawo karancin abincin, saboda haka rabar da shi da wuri; zai yi matukar taimakawa wajen wadata kasar da abinci”, in ji ta.
Har ila yau ta ci gaba da cewa, “Kusan zan iya cewa, kashi dari bisa dari na manoman da aka rabawa wannan taki a halin yanzu, sayar da shi za su yi; kodai don su yi girbi ko kuma su yi wani abu daban da kudin, babban abin haushin ma shi ne; ‘yan kasuwa za su sayarwa a rahusa, wanda kuma lokacin da suke bukatar takin; sai ‘yan kasuwar sun rubanya musu kudin a kan yadda suka sayar musu”.
Bugu da kari, ya kamata gwamnati ta rika tuntubar manoma; don sanin lokacin da ya fi dacewa a raba musu wannan taki, domin gujewa ci gaba da fuskantar wannan matsala.
Aisha ta sake yin nuni da cewa, rashin rabar da takin a kan lokaci na kara barazanar haifar da karancin abinci a fadin kasar, musamman ma a wannan yanki namu na Arewa, domin kuwa mene ne amfanin a ce ana rabar da shi; musamman a Kaduna a cikin watan takwas? Sannan, kyautuwa ya yi gwamnati ta samu manyan sito-sito a zuba takin a ciki ta yadda a watan Junairu ko na Fabrairun badi; ta za fito da shi a raba wa manoman, domin ta haka ne kadai takin zai yi wa manoman amfani.
Kazalika, ya kamata kowane manomi a ba shi akalla buhu biyar na wannan taki; sabanin irin rabon da gwamnatin jihar ta yi a bana na rabon buhu biyu-biyu, saboda haka idan dai don Allah ne ake so a yi, ya zama wajibi a gyara; domin su manoma da yanayi suke tafiya da kuma yawan adadn takin da suke bukata, don fara yin nomansu.
Har wa yau, wasu ma wadanda gwamnatin jihar ta rabawa takin, ba su ma san ko hanyar zuwa gona ba; shi yasa a Nijeriya muke cikin irin wannan hali har zuwa yanzu, don haka ka ga da muguwar rawa, gwamma kin tashi, in ji Aisha.
Musa Bala, shi ma wani sanannen manomi ne a jihar ta Kaduna, sannan kuma tsohon shugaban kungiyar masu kiwon kajin gona; reshen Jihar Kaduna (PAN).
Bala ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi, musamman gwamnatocinmu na Arewa da cewa; a duk lokacin da za su rabar da takin zamani, su rika rabawa daga farkon watan Junairu zuwa na Fabrairu, idan kuma an dade shi ne zuwa watan uku.
Ya kara da cewa, raba musu takin a kan lokaci; shi ne zai ba su damar sanin irin yanayin aikin da za su yi a gonakinsu, amma idan har takin bai kai ga a hannunsu a kan lokaci ba; ba za su iya sanin irin yanayin aikin da za su yi a gonakin nasu ba.
Don haka, rabar da wannan taki a kurarren lokaci; musamman yadda wasu gwamnatocin Arewacin Nijeriya ke yi, ba zai taba haifar wa da manoma da mai ido ba.
Har ila yau, Malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Kaduna polytechnic), kuma fitaccen mai fashin baki a kan tattalin arzikin kasa, Dakta Abdullahi Umar Gwandu, shi ma ya bayyana cewa; matakin da gwamnatin tarayya da sauran gwamnatocin jihohi suka dauka na raba wa manoma takin zamani, mataki ne da ya dace.
Sannan kuma ya yi nuni da cewa, gwamnati ta damu da halin da manoma suke ciki, domin kuwa ta bayar da tata gudunmawar kai tsaye wajen samar da abinci; domin taki yana cikin abubuwan da suke ci wa manoma kudi, yake kuma wahalar da su.
Domin kuwa a halin yanzu, taki mai arhana shi ne wanda kudinsa ya kai Naira 40,000 zuwa sama. Kazalika, wasu ma rabar da takin suka yi kyauta ga manoma.
Sai dai, ba a nan gizon yake saka ba; kullum muna kira ga gwamnati cewa, duk abin da za a yi wa mutane; a tabbata an yi musu a kan lokacin da ya dace, dalili kuwa aikin noma musamman na damina; abu ne da yake da lokaci.
Saboda haka, idan aka duba a nan Arewa; damina na tsayawa ne tun a cikin watan hudu zuwa watan biyar, a lokacin ne manoma suka fi bukatar kayan aiki, wanda kuma takin zamani na cikinsu.
Amma abin mamaki shi ne, mafi yawancin jihohin nan; sun raba takin nan a cikin watan takwas, kamar Jihar Kaduna; ita sai yanzu ma take yin nata rabon takin.
Magana ta gaskiya, duk wani manomi na gaskiya; ba manomin gidan Rediyo ba, mafi yawansu sun gama aiki kuma bukatar takin nan ta ragu.
Misali, idan ka dauki Masara, akasarin manomanta, sun gama amfani da taki, haka nan mafi yawan manonan Shinkafa da Dawa su ma duk sun gama amfani da taki, to yanzu an zo ana ba su taki, ko da kuwa kyauta ne, takin kusan ba shi da wani amfani a gurinsu, in ji shi.
Dakta Gwandu ya ci gaba da bayyana cewa, mafi akasarin abin da ke faruwa shi ne, wadanda ake bai wa takin yanzu, wasunsu su kan sayar da shi ne; domin yin wasu ayyukan, wasu kuma masu hali a cikin manoman; su kan ajiye shi har zuwa badi ko kuma su yi noman rani da shi.
Don haka, abun da muke kira ga gwamnati a nan shi ne, duk abin da za ta yi; ta yi kokari ta yi shi a lokacin da ya dace. Sannan kuma, akwai zarge-zarge da dama na cewa; ‘yan siyasa kadai ake bai wa takin, ba ainahin manoma ba.
Sau tari, haka za ka ga ana raba wa ‘yan siyasa wannan taki; wadanda kwata-kwata ma ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da wannan noma, wani a ba shi tan daya na takin; wani ma ka ga an ba shi Tirela guda.
A karshe, ya kamata gwamnati ta yi gyara a kan wannan lamari, amma ba a ce har an shiga watan takwas, ba a ma gama rabon wannan taki ba, kusan za a iya cewa; hakan ya zama abin da ake kira da tubka da warwara, in ji Daktan.