Wake na daya daga cikin cimar akasarin ‘yan Nijeriya, duba da cewa yana daya daga cikin abinci mai gina jikin Dan’adam. Wannan dalili ne ya sa a kauyuka da birane al’umma da dama ke noman sa, domin amfanin gida da kuma sayarwa a kasuwanni.
Sai dai, wasu manoman ba sa bin hanyar da ta dace wajen noman wannan Wake. Domin kuwa, a Nijeriya girbin da ake samu har yanzu bai wuce kasa da tan 0.2 a kowace hekta daya, duk da cewa kuma; masu yin nomana Waken ta hanyar da ta dace, sukan iya girbe kimanin tan 2 a kowace hekta guda.
Watannin da suka fi dacewa a noma Wake a kasar nan, na farawa ne daga watan Mayu zuwa na Yuni.
Kazalika, dangane da yanayin kakar damina; ana kuma yin nomansa daga watan Mayu, Yuni da kuma na Yuli.
Babu shakka, nomansa a cikin wadannan watanni; zai sa ya samu isasshe ko kuma wadataccen ruwa.
Haka zalika, wadanda ke noman wannan Wake a lokacin rani; za su iya shuka Irinsa a kowane irin lokaci.
Watannin da suka fi dacewa a shuka Wake a Nijeriya sun hada da watan Afirilu, Mayu, Yuni, Juli, Augusta, Satumba har kuma zuwa Disamba.
Watan Afirilu:
A kudancin Nijeriya, ana fara shuka Irin Wake a watan Afirilu, sakamakon cewa a wannan wata ne ake fara yin ruwan sama.
Har ila yau, a cikin watan ne kuma Irin Waken da aka shuka; galibi ba a cika samun wata matsala kamar ta kwarin da ke lalata amfanin gona ko wani abu makamancin haka ba.
Watan Mayu:
A Nijeriya, musamman a yankunan da suke da dausayi ne ake fara samun ruwan sama, wanda hakan ya sa watan ya kasance, lokacin da ya fi dacewa a shuka Irin Waken.
Kazalika, a cikin watan ne Waken da aka shuka zai yi girma sosai; domin ba a cika samun kwarin da suke lalalata amfanin gonar ba.
Watan Yuni:
Shi ma wannan watan, na daya daga cikin watan da ya dace a shuka Irin Wake a kudancin Nijeriya da kuma Arewacin kasar. Domin kuwa, a cikin watan ba a cika samun kwarin da ke lalata amfanin gonar ba.
Watan Yuli:
Shi ma wannan watan, na daya daga cikin watannin da suka dace a noma Wake, musamman a kudancin wannan kasa, a kuma cikin watan; ba a cika samun kwarin da ke lalata amfanin ba.
Watan Augusta:
Musamman a kudancin Nijeriya, wannan watan na da matukar kyau a shuka Irin Wake, sai dai ana kuma bukatar manomi ya kasance ya tanadi kayan ban ruwan da zai yi wa Waken.
Haka nan, a Arewacin Nijeriyar; ganin cewa a watan ne ake samun ruwan sama mai yawa, watan ya kasance mafi kyau na shuka Irin Waken.
Watannin Satumba zuwa na Disamba:
Zai iya yiwuwa, Wake ya girma a cikin wadannan watanni har zuwa cikin watan Oktoba.
Daga watan Satumba zuwa Disamba, nan ne kakar rani ke fara kunnu kai; inda kuma za a iya samun bullar kwarin da ke lalata amfanin gona, wanda a cikin watannin ne kuma ake so manomi ya rika amfani da magungunan kashe kwari.