Kungiyoyin Manoma a jihar Nasarawa za su amfana da tallafin dalan Amurka 25,000 domin bunkasa harkar Noma a fadin jihar.
Da yake jawabi kan kan lamarin, Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya ce; Bankin Duniya tayi alkawarin baiwa al’umomin dake kauyaka goma tallafi domin gudanar da aikin gona da samar da wadacecen abinci.
- Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Rabon Kayayyakin Amfanin Gona Ga Manoman Kaduna 40,000
- Mozambique: An Shirya Maido Da Noman Alkama Bisa Tallafin Fasahohin Kasar Sin
Ya ce; kauyuka guda goma dake Jihar Nasarawa da za su amfana da wannan tallafin sun hada da manoman dake Karamar Hukumar Doma da na Karamar Hukumar Toto.
Gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da yakewa manoma jawabi a ziyarar da yakai garin Do-ma.
Gwamnan ya ce; kuddurin Gwamnatinsa na ganin jihar Nasarawa ta yi wa sauran jihohi fincin kau wajen samar da wadacecen abinchi mai gina jiki a Nijariya yasa.
A makon da ya gabata Gwamnatinsa ta rabawa manoma motochin noma guda 23 da tallafin kudi naira dubu goma ga dumbin manoma domin karfafa masu giwa.
Gwamnan ya ce yana tare da kungiyoyin manoma a koda yaushe. Kuma Gwamnati tana samar da abubuwan more rayuwa ga Kananan manoma a jihar.
Ya Kara da cewa jajurcewar da Gwamnatinsa keyi wajen ganin manoma sun tsayu da kafafunsu, gashi Bankin Duniya tare da hadin giwar Bankin raya harkan noma ta Afirka da Gwamnatin jihar sukaga cancantar manoman jihar Nasarawa aka fara basu wannan tallafin na &25,000 ga ko wani kauye har kauyuka goma.
Shi ma a nasa jawabin Shugaban Kungiyar ACReSAL Dr. Joy Iganya Agene ya ce; kimanin manoma 620 ne za su amfana da tallafin wannan kudin domin bunkasa harkar noma a jihar.
Ya ce; shirin ya hada maza da mata bai ware wasu jinsin ba. A madadin haka mata kimanin 367 ne zasu amfana da wannan tallafin.
Maza kimanin 253 ne za su amfana da wannan tallafin.
Shi ma a nasa jawabin Sarkin Doma Alihaji Aliyu Ogah (Andoma na Doma) ya yi godiya da Gwamna Abdullahi Sule dake samar da kuddurin cigaban al’umman jihar Nasarawa a koda yaushe.
Sarkin ya yi kira ga al’umman Karamar Hukumar Toto da Doma da zasu ci gajiyar wannan tal-lafin dasu zage dantse su yi amfani da kudaden ta anyar noma da al’umman Kasa zasu amfana.
Sannan ya yi godiya ga wadanan kungiyoyin dama Bankin Duniya da ya tallafima al’umman ji-har.