Kimanin manona 100 ne suka amfana da horon da Cibiyar da ke kula da fitar da amfanin gona zuwa kasar waje NEPC ta gudanar a karamar Obi da ke a jihar Nasarawa.
An horas da manoman ne, kan dabarun zamani kan yadda za su fitar da Doyar da suka noma zuwa ketare.
- Masanin Tattalin Arziki: Kasar Sin Ce Karfin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
- Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?
Jami’ar hukumar da ke a ofishin karamar Cibiyar Lafia a cikin Amina Abdullahi Tumba ce ta kadamar da bayar da horon.
Horon na kwana daya, an bude shine a shalkwatar Agyaragu, sa ke a gundumar raya karkara ta Jenkwe da ke a cikin jihar.
Aminca a hawabinta a wajen horon ta bayyana cewa, manufar horon da aka shirya wa manoman na Doyar a jihar ta Nasarawa, an shirya masu ne domin su zamo akan gaba a daukacin fadin kasar nan wajen yin noman na Doyar.
A cewar Amina, jihar ta Nasarawa ta kasance ta na da kyakyawar kasa mai albarka wajen yin noma
Jami’ar ta kuma yi kira ga manoman na Doyar da suka amfana da dabarun horon na noman na zamani lokacin horon su kara bunkasa nomansu na Doyar.
A kasidar da ya gabatar a wajen horon wani kwarare a fannin aikin noma William Akaamaa ya yi kira ga manoman na Doyar da ke a cikin jihar, da su dinga tuntubar kwararru a fannin aikin naoma ako da yaushe, musamman domin su kara habaka noman na sun a Doyar, da kuma aminta da ita a kasuwannin duniya.
A na sa bangaren Daraktan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC reshen jihar Babatunji Omoyeri yay i jawabi ne akan mahimancin da ke tattare da fitar da amfanin gona zuwa kasuwanin duniya domin sayarwa
Babatunji ya kuma shawarci manoman da su tabatar da suna bin dukkan ka’idojin da aka gindaya na fitar da Doyar da suka noma zuwa kasuwar duniya, musamna domin kar a dinga kin amincewa da ita idan an fitar da ita wajen.
Shi ma a na sa jawabin a gurin bayar da horon kwamishinan aikin noma da albarkatun Ruwa na jihar Nuhu Ibrahim Oshafu, godewa Cibiyar ta NEPC ya yi kan shiryawa manoman na Doyar horon.
Oshafu ya kuma bai wa Cibiyar tabbacin cewa, gwamnatin jihar a shirye take ta yi hadaka da Cibiyar, domin a kara bayar da kwarin guiwa wajen kara bunkasa noma a jihar musaman, ba wai noman Doya kawai ba, har da sauran amfanin gona.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp